TAMBAYA TA 098 LIMANCIN MAI NAƘASA As-Salaamu Alaikum, Maigida ne yake da naƙasar da take hana shi yin sallah a tsaye, to yaya limancinsa ga iyalinsa da waɗanda ba su kai shi ƙwarewa ko zurfi a cikin karatun Alqur’ani ba? AMSA A098 Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah. Malamai sun sha bamban a kan limancin mara lafiya ko mai wata naƙasa a jikinsa ga masu lafiya, waɗanda ba su da irin wannan naƙasar. Waɗansu sun ce makaruhi ne, waɗansu kuma sun ce ya halatta. As-Shaikh Al-Mujaddid Al-Albaaniy (Rahimahul Laah) ya ce: Babu yadda za a ce yin hakan makaruhi ne, balle ma har a ce wai sallar ba ta inganta ba saboda hakan, matuƙar dai sharuɗɗan Limancin da aka shimfiɗa sun cika a kansa. Ba mu ganin wani bambanci a tsakanin limancinsa da limancin makaho wanda ba ya iya tsare kansa daga najasa irin yadda mai gani yake iya tsarewa. Haka kuma mai sallah a zaune wanda ya kasa miƙewa tsaye. Domin dai kowannensu ya aikata irin abin da yake iyawa ne da gwargwadon ikonsa kawai, kuma da ma...