Skip to main content

LIMANCIN MAI NAKASA

TAMBAYA TA 098

LIMANCIN MAI NAƘASA

As-Salaamu Alaikum,

Maigida ne yake da naƙasar da take hana shi yin sallah a tsaye, to yaya limancinsa ga iyalinsa da waɗanda ba su kai shi ƙwarewa ko zurfi a cikin karatun Alqur’ani ba?

AMSA A098

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Malamai sun sha bamban a kan limancin mara lafiya ko mai wata naƙasa a jikinsa ga masu lafiya, waɗanda ba su da irin wannan naƙasar. Waɗansu sun ce makaruhi ne, waɗansu kuma sun ce ya halatta. As-Shaikh Al-Mujaddid Al-Albaaniy (Rahimahul Laah) ya ce:

Babu yadda za a ce yin hakan makaruhi ne, balle ma har a ce wai sallar ba ta inganta ba saboda hakan, matuƙar dai sharuɗɗan Limancin da aka shimfiɗa sun cika a kansa. Ba mu ganin wani bambanci a tsakanin limancinsa da limancin makaho wanda ba ya iya tsare kansa daga najasa irin yadda mai gani yake iya tsarewa. Haka kuma mai sallah a zaune wanda ya kasa miƙewa tsaye. Domin dai kowannensu ya aikata irin abin da yake iyawa ne da gwargwadon ikonsa kawai, kuma da ma:

Allaah ba ya ɗora wa wani rai komai face dai iyawarsa
Surah Al-Baqarah: 286.

Daga cikin sharuɗɗan da malam yake nufi a nan akwai abin da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ambata a cikin hadisin Muslim: 673, cewa:

Wanda zai yi wa mutane limanci shi ne wanda ya fi su karatun littafin Allaah; idan kuma sun zama daidai a karatun sai wanda ya fi su sanin Sunnah; idan kuma sun yi daidai a Sunnah sai wanda ya riga su yin hijira; idan kuma sun zama daidai a hijira to sai wanda ya riga su musulunta.

A wata riwaya kuma ya ce: Wanda ya fi su a shekaru, maimakon: Wanda ya riga su musulunta.

Sannan kuma ƙa’idar da malamai suka shimfiɗa a wurin limanci ita ce: Duk wanda sallarsa ta inganta ga kansa in yana shi kaɗai, to limancinsa ta inganta ga waninsa.

Idan limamin ya yi sallarsa a zaune, a nan ma malamai sun sake shan bamban game da mamu masu yin sallah a bayansa. Shin ko su ma a zaunen za su yi ko kuwa a tsaye tun da ba su da uzuri ko larura irin ta sa?
Sahihiyar maganar da muka fi natsuwa da ita ita ce:

Idan tun farko limamin ya fara sallar a zaune ne, to wajibi ne masu sallah a bayansa su ma su yi sallar a zaune tun daga farko har ƙarshe, saboda umurnin Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da ya ce:

Ku yi koyi da limamanku: Idan ya yi sallah a tsaye to ku yi sallar a tsaye ku ma; idan kuma ya yi sallah a zaune sai ku ma ku yi sallar a zaune. (Muslim: 417)

Amma idan ya fara sallar a tsaye ne sai kuma daga baya wata larura ta sanya shi ya zauna, to a nan ba sai mamu sun zauna ba. Suna iya cigaba da sallarsu a bayansa a tsaye. Domin a lokacin da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya fito a cikin rashin lafiyarsa na ajali ya tarar Abubakar yana cikin sallah tare da sahabbai, sai ya zauna a gefensa na hagu a matsayin liman kuma Abubakar ya koma mamu tare da sauran sahabbai. A wannan lokacin shi Abubakar da sauran mutane sun cigaba da yin sallah a tsaye ne a bayan Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), wanda yake yin sallah a zaune, kuma bai umurce su da su zauna ba. (Al-Bukhaariy: 198; Muslim: 418).

Sannan kuma malamai sun nuna cewa: Idan limamin ya yi sallarsa da nuni (imaa’i ko ishara) a wurin ruku’u ko sujada saboda larura, to su mamu sai dai su cika su daidai, ba za su yi nuni irin na limamin ba. (Tamaamul Minnah: 1/340).

Allaah ya ƙara mana fahimta a cikin addininmu.

Wal Laahu A’lam.
26/5/2019
3: 34pm.

*Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
08164363661

Comments

Popular posts from this blog

BARKA DA HUTUN ƘARSHEN MAKO

 BRANCOSIYYA HALARCI Alhaji Auwal Branco tare damu masoyansa, munawa Al'umma Barka da ƙarshen mako. Allah ya cikawa kowa burinsa. Muyi Branco da farar Zuciya #Branco2020 Muneer Yusuf Assalafy 08/08/2020

NASARA DAGA ALLAH

TSARIN MU NA KADUNA 'Ya'yan Jam'iyyar PDP na Zone 2 sun gamsu da riqon Shehu Giant shiyasa suke cewa so ✌ ne. Kaf matasan PDP dake Kaduna sun gamsu da Hon Aliyu Bello, hakan tasa muke cewa PDP Youth leader dan bello so ✌ ne. 'Yan PDP na Kaduna North Mun gamsu Mun amin ce da sauyin shugabanci, hakan yasa mukace Branco mukeso domin ya cancanta. Kawo Constituency kuwa maganar Sa'eed Usman Gombe ake a ko ina, domin cancantarsa da nagartarsa. Badarawa/Malali ward ko san barka 'yan PDP sukeyi da wakilcin Zayyanu Sa'eed Malali. Allah ya bamu nasara Muneer Yusuf Assalafy Zonal Coordinator Northwest Atiku 2023 Project Rescue Nigeria 06/07/2020

HADA SALLAH SABODA RUWAN SAMA

*TAMBAYA TA 100*  *HAƊA SALLAH SABODA RUWAN SAMA*  _As-Salaam Alaikum,_ Ranar Asabar bayan faɗuwar rana muka kai ƙarshen azumi na 13 a wannan shekara ta 1440 bayan Hijira. Mun ci dabino, mun kurɓi ruwa, kuma muka yi addu’ar shan-ruwa: *Zahabaz Zama’u, Wab Tallatil Uruuq, Wa Thabatal Ajru in shaa’al Laah* kafin mu fita zuwa sallar Maghrib a masallacin farko a layinmu: Layin Masallaci, Sabon Kawo Kaduna. Bayan sallame sallar Magrib sai liman ya miƙe, ladan kuma ya fara tayar da iƙamar sallar isha’i, da manufar a haɗa sallolin kenan, *Jam’u-Taqdeem.* A nan ne sai wasu mutane da suke sallah a wajen masallacin suka fara faɗin: *Ba hadari fa!* *Ba ruwan sama fa!* Amma liman bai saurare su ba, har aka kammala sallar. Sannan ko da aka sallame sallar ma bai ce komai a kan wannan matsalar ba. Don haka, na ga ya dace in yi amfani da wannan kafar in ce wani abu ko da a taƙaice a kan mas’alar. 1. Haɗa salloli biyu da suka yi tarayya a lokaci (Azahar da La’asar ko kuma Magrib da Ish...