*TAMBAYA TA 100* *HAƊA SALLAH SABODA RUWAN SAMA* _As-Salaam Alaikum,_ Ranar Asabar bayan faɗuwar rana muka kai ƙarshen azumi na 13 a wannan shekara ta 1440 bayan Hijira. Mun ci dabino, mun kurɓi ruwa, kuma muka yi addu’ar shan-ruwa: *Zahabaz Zama’u, Wab Tallatil Uruuq, Wa Thabatal Ajru in shaa’al Laah* kafin mu fita zuwa sallar Maghrib a masallacin farko a layinmu: Layin Masallaci, Sabon Kawo Kaduna. Bayan sallame sallar Magrib sai liman ya miƙe, ladan kuma ya fara tayar da iƙamar sallar isha’i, da manufar a haɗa sallolin kenan, *Jam’u-Taqdeem.* A nan ne sai wasu mutane da suke sallah a wajen masallacin suka fara faɗin: *Ba hadari fa!* *Ba ruwan sama fa!* Amma liman bai saurare su ba, har aka kammala sallar. Sannan ko da aka sallame sallar ma bai ce komai a kan wannan matsalar ba. Don haka, na ga ya dace in yi amfani da wannan kafar in ce wani abu ko da a taƙaice a kan mas’alar. 1. Haɗa salloli biyu da suka yi tarayya a lokaci (Azahar da La’asar ko kuma Magrib da Ish...
Comments
Post a Comment