*TAMBAYA TA 093*
*AZUMIN BANA YA ZO, ANA BIN TA NA-BARA*
_As-Salamu Alaikum,_
Tun bara kafin ta yi aure ake bin ta azumma guda shida ba ta rama ba, har ga shi kuma wannan azumin na bana ya zo. Yaya za ta yi kenan?
*AMSA A093*
_Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah._
Abin da Shari’ar Musulunci ta faɗa dangane da waɗanda suka kasa yin azumi saboda larura irin ta tsufa ko dai wani rashin lafiya dawwamamme, ko kuma saboda larurar ciki ko shayarwa shi ne: Ciyar da abinci ga talaka a maimakon duk yini guda da ba su iya yin azumin a cikinsa ba. Allaah Ta’aala ya ce:
*Kuma abin da yake a kan waɗanda suke ɗaukarsa da wahala shi ne fansa: Ciyar da abinci ga musakai.*
_Suratul Baqarah: 184._
Kuma waɗanda suka kasa yin azumin saboda larurar rashin lafiya, ko don suna cikin halin tafiya, ko saboda haila ko jinin haihuwa *(nifaas)* shi ne: Su lissafe ranakun da ba su yi azumin a cikinsu ba, daga baya kuma idan sun dawo daga tafiyar ko idan sun samu lafiya, sai su biya a cikin waɗansu ranakun na daban, kamar yadda Allaah ya ce:
*Kuma duk wanda ya zama mara lafiya ko a cikin halin tafiya, to sai ya biya adadin waɗansu ranaku na daban.*
_Suratul Baqarah: 185._
Wanda kuma bai iya ramawa ba har wani azumin ya zo ya samu na baya, duk da haka dai ana bin sa bashin waɗancan ɗin. Kuma abin da zai yi, in ji malamai shi ne: Ya fara gabatar da waɗancan basussukan kafin shigowar watan wannan Azumin.
Idan kuma ba zai iya ba, to sai ya bar ramuwar har sai bayan an kammala wannan azumin.
Sannan kuma wajibi ne ya tuba ga Allaah _Tabaaraka Wa Ta’aala_ a kan wannan jinkirin da ya yi, matuƙar dai da gangar ko da sakaci ne ya bari har wannan azumin ya zo bai rama waɗancan ba.
Amma idan ba da sakaci ba ne, to babu wani laifi a kansa, sai dai kawai ya rama su ɗin a bayan an gama wannan azumin.
Allaah ya datar da mu gaba-ɗaya ga aikata abin da yake so kuma yake yarda da shi.
_Wal Laahu A’lam._
_18/05/2019_
_6: 25am._
*Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
Majlisin sunnah
08164363661

Comments
Post a Comment