TAMBAYA TA 096
ADDU’A A KOWACE RANAR AZUMI
As-Salaamu Alaikum,
Malam, shin yaya matsayin irin addu’o’in da ake turo wa mutane a kan kowane kwanakin Ramadan da kalar addu’ar da mutum zai yi?
AMSA A096
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.
Ai ba ma addu’a ba ce kaɗai. Wasu har da irin nafilar sallar da za a yi a kowace rana ko dare na Ramadan, da kuma irin abin da za a karanta a kowace raka’a suke yaɗawa! Waɗannan duk suna daga cikin ƙirƙirarrun al’amura ne a cikin addini, bayan wucewar mutanen kirki. Domin babu wata aya ko wani hadisi sahihi da ya tabbatar da su. Kuma da ma musulunci, kamar yadda manyan malamai irin su Ibn Al-Qayyim (Rahimahumul Laah) suka faɗi, shi ne: Maganar Allaah da maganar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallaam) kaɗai, sai kuma maganar Sahabbai (Radiyal Laahu Anhum).
Abin da ya tabbata a cikin Sunnah Sahihiya shi ne yawaita ayyukan alkhairi a cikin Ramadan, kamar tilawar Alqur’ani, sauraron tafsirinsa, ƙara fahimtarsa, sallolin nafila, addu’o’i, sadaka, sada zumunci da sadar da alkhairi ga jama’a, da sauransu. A wurin sallar ba a ce a keɓance irin surori ko adadin raka’o’in kowace raka’a ba, haka kuma ba da keɓance wani nau’i ko lafazin addu’o’in kowane rana ko dare ba. Malamai kuma sun yarda cewa: Daga cikin hanyoyin da Bidi’a ke saɗaɗowa ta shiga cikin addini, akwai: Duk ibadar da Allaah ko Manzonsa suka sake ta haka nan ba da ƙaidi ba, sai kuma wani ko wasu su yi mata ƙaidi da wuri ko lokaci ko adadi!
Mun dai riga mun san cewa: Dukkan bidi’a ɓata ce, kamar yadda Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallaam) ya yi bayaninsa a cikin hadisai sahihai, kamar hadisin Al-Irbaad Bn Saariyah (Radiyal Laahu Anhu) wanda Abu-Daawud da At-Tirmiziy da Ibn Maajah suka fitar da shi, cewa:
Watarana Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallaam) ya yi mana limancin sallah [Sallar Asubah], sai kuma ya fuskanto mu ya yi mana wa’azi mai ratsa jiki, wanda ya sa idanu suka zubar da hawaye kuma zukata suka ƙara tsoro, sai wani mutum daga cikin Sahabbansa ya ce: Ya Manzon Allaah! Kamar wa’azin mai ban-kwana?! To, ka yi mana wasiyya mana! Sai ya ce: {Ina yi muku wasiyya da jin tsoron Allaah, kuma da ji da biyayya ko da kuwa bawa ne Bahabashe aka shugabantar a kanku, domin daga cikinku duk wanda ya yi tsawon rayuwa a bayana to kuwa zai ga saɓani mai yawa. Don haka, sai ku kama Sunnata da Sunnar Halifofin nan Shiryayyu, tabbatattu a kan shiriya a bayana, kuma ku damƙe ta da turamen haƙora. Kuma ku yi nesa da ƙirƙirarrun al’amura, domin kowace ƙirƙira bidi’a ce, kuma kowace bidi’a ɓata ce}.
A cikin wata riwaya ta An-Nasaa’iy ya ce: {Kuma kowace ɓata tana cikin Wuta}.
(Dubi ƙarin bayanin wannan hadisin a cikin Sharhin Al-Arba’uunas Salafiyyah # 3)
Allaah ya datar da mu ga yin riƙo da sunnah da nisantar bidi’a.
Wal Laahu A‘lam
26/5/2019
2: 03
*sheikh Muhammad Abdullah Assalafy*
Majlisin sunnah
Comments
Post a Comment