Skip to main content

Posts

MAI DOKAR BACCI

A jihar Kaduna idan akwai wanda zamuce ya kawo korona bai wuce gwamna El-rufai, domin shine wanda aka fara samu da ita. A jihar Kaduna ne gwamnan ya hana musulmai sallah tsawon wata 4. A jihar Kaduna ne gwamnan ya hana kiristoci zuwa coci tsawon wata 4. Har yanzu a jihar ne musulmai basu zuwa khamsu salawat da aka saba guda biyar, kuma har yanzu a jihar ne ya hana buɗe coci a ranar Saturday. A tsakiyan faruwar hakan, gwamnan yace bazaije masallaci ba domin ya tsufa kada korona ta kamasa. A lokacin ne gwamna ya bude masallacin juma'a da coci ranar Sunday tare da sharaɗin Social distance. A lokacin ne kuma gwamnan da takwarorinsa suka haɗa gangamin taron kamfen na mutane sama da dubu goma. Anya gwamnan Kaduna ba amso kwangilar rusa addinai yayi ba kuwa? Koma dai menene Allah na nan fir'auna ma yayi ya wuce sai dai tarihi. ✍🏿 Muneer Yusuf Assalafy 10/08/2020
Recent posts

BARKA DA HUTUN ƘARSHEN MAKO

 BRANCOSIYYA HALARCI Alhaji Auwal Branco tare damu masoyansa, munawa Al'umma Barka da ƙarshen mako. Allah ya cikawa kowa burinsa. Muyi Branco da farar Zuciya #Branco2020 Muneer Yusuf Assalafy 08/08/2020

BRANCOSIYYA HALARCI

Branco Mai Allah. Mufa masoyan Branco duk inda ka ganmu cikin kwanciyar hankali muke. Mun sallamawa ubangiji mai bayarwa, shi muke roqon ya bamu Branco muke yau ko gobe ko yanzu-yanzu, ba gudu ba ja da baya. Muyi Branco da farar Zuciya ✍🏿 Muneer Yusuf Assalafy 06/08/2020

TAFIYAR NASARA

Cancanta da iya mulki a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP a zone 2, bamu da kamar Mai girma Hon Shehu Giant Hakan tasa mukace  so ✌️a zone 2, babu canji. Kaduna north kuwa canji muke bukata gurin Allah, mun gaji da riƙon sakainar kashi da akewa PDP. Hakan tasa mukace Branco ne da yardan Allah, bisa cancanta da nagartarsa. Hon Auwal Branco shine zabin Al'umma Allah ya bamu nasara #giant2020 #branco2020 Allah ya bamu nasara ✍🏿 Muneer Yusuf Assalafy 27/07/2020

BRANCON DAI

Mutane sukace: Muneer wai Branco baida abokin takara ne? Nace: menene yasa kuke min tambayar nan. Sukace: Munga kaso 99 na matasan PDP dake Kaduna North waɗanda ke  facebook/twitter duk tallan Branco suke. Nace: yo ai shi Branco yin Allah ne, kuma idan rana ta fito ai tafin hannu baya kareta. Muyi Branco da farar Zuciya. #Branco2020 ✍🏿 Muneer Yusuf Assalafy Zonal Coordinator Northwest Atiku 2023 Project Rescue Nigeria 26/07/2020

NASARA DAGA ALLAH

TSARIN MU NA KADUNA 'Ya'yan Jam'iyyar PDP na Zone 2 sun gamsu da riqon Shehu Giant shiyasa suke cewa so ✌ ne. Kaf matasan PDP dake Kaduna sun gamsu da Hon Aliyu Bello, hakan tasa muke cewa PDP Youth leader dan bello so ✌ ne. 'Yan PDP na Kaduna North Mun gamsu Mun amin ce da sauyin shugabanci, hakan yasa mukace Branco mukeso domin ya cancanta. Kawo Constituency kuwa maganar Sa'eed Usman Gombe ake a ko ina, domin cancantarsa da nagartarsa. Badarawa/Malali ward ko san barka 'yan PDP sukeyi da wakilcin Zayyanu Sa'eed Malali. Allah ya bamu nasara Muneer Yusuf Assalafy Zonal Coordinator Northwest Atiku 2023 Project Rescue Nigeria 06/07/2020

N-POWER A NIGERIA

N-POWER KO RASHIN AIKI KO MUTUWAR ZUCIYA? Hukumar N-power sun qiyasta mutum 100 na rijista duk second daya. Hakan yana faruwa ne sbd qarancin rashin aikinyi a Lafjeriya, da yawan wadanda suka gama jami'a basu da abinyi, hakan tasa aka bude N-power domin su rinqa samun albashi da zai rage musu talauci. Ga matashin da yasan abinda yake, sam bai kamata ya bari zuciyar sa ta mutu ba wajen neman N-power musamman ga 'yan sakandare. Matasa kada ku bari zuciyar ku ta mutu wajen neman N-power, ku tashi ku nema na kanku ko zaku rufawa kanku asiri. Abin takaici shine hatta 'yan sakandare ma zuciyar su ta mutu suna jiran su samu na gwamnati, a lokacin da abokansu suke aikin hannu suna samun manyan kudi. Kaba kanka amsa ga wadannan tambayoyin yakai dan sakandare da ka cike N-power 1. Shin kudin da zasu baka zai cireka a talauci? 2. Shin dubu goma da za a baka duk Wata zai isheka aure? 3. Dubu goma da za a baka zai Isa kasai gida? 4. Dubu goma da za a baka zai isa Kas...