Skip to main content

N-POWER A NIGERIA

N-POWER KO RASHIN AIKI KO MUTUWAR ZUCIYA?

Hukumar N-power sun qiyasta mutum 100 na rijista duk second daya.

Hakan yana faruwa ne sbd qarancin rashin aikinyi a Lafjeriya, da yawan wadanda suka gama jami'a basu da abinyi, hakan tasa aka bude N-power domin su rinqa samun albashi da zai rage musu talauci.

Ga matashin da yasan abinda yake, sam bai kamata ya bari zuciyar sa ta mutu ba wajen neman N-power musamman ga 'yan sakandare.

Matasa kada ku bari zuciyar ku ta mutu wajen neman N-power, ku tashi ku nema na kanku ko zaku rufawa kanku asiri.

Abin takaici shine hatta 'yan sakandare ma zuciyar su ta mutu suna jiran su samu na gwamnati, a lokacin da abokansu suke aikin hannu suna samun manyan kudi.

Kaba kanka amsa ga wadannan tambayoyin yakai dan sakandare da ka cike N-power

1. Shin kudin da zasu baka zai cireka a talauci?

2. Shin dubu goma da za a baka duk Wata zai isheka aure?

3. Dubu goma da za a baka zai Isa kasai gida?

4. Dubu goma da za a baka zai isa Kasai mota ko mashin?

Shin abokanka nawa ka sani masu aikin hannu da suka mallaki abinda na ambata ta hanyar aikin hannu?

Abokina ka tashi ka nema kawai yafi maka N-power

Allah ya datar damu

Muneer Yusuf Assalafy
29/06/2020

Comments

Popular posts from this blog

BARKA DA HUTUN ƘARSHEN MAKO

 BRANCOSIYYA HALARCI Alhaji Auwal Branco tare damu masoyansa, munawa Al'umma Barka da ƙarshen mako. Allah ya cikawa kowa burinsa. Muyi Branco da farar Zuciya #Branco2020 Muneer Yusuf Assalafy 08/08/2020

NASARA DAGA ALLAH

TSARIN MU NA KADUNA 'Ya'yan Jam'iyyar PDP na Zone 2 sun gamsu da riqon Shehu Giant shiyasa suke cewa so ✌ ne. Kaf matasan PDP dake Kaduna sun gamsu da Hon Aliyu Bello, hakan tasa muke cewa PDP Youth leader dan bello so ✌ ne. 'Yan PDP na Kaduna North Mun gamsu Mun amin ce da sauyin shugabanci, hakan yasa mukace Branco mukeso domin ya cancanta. Kawo Constituency kuwa maganar Sa'eed Usman Gombe ake a ko ina, domin cancantarsa da nagartarsa. Badarawa/Malali ward ko san barka 'yan PDP sukeyi da wakilcin Zayyanu Sa'eed Malali. Allah ya bamu nasara Muneer Yusuf Assalafy Zonal Coordinator Northwest Atiku 2023 Project Rescue Nigeria 06/07/2020

HADA SALLAH SABODA RUWAN SAMA

*TAMBAYA TA 100*  *HAƊA SALLAH SABODA RUWAN SAMA*  _As-Salaam Alaikum,_ Ranar Asabar bayan faɗuwar rana muka kai ƙarshen azumi na 13 a wannan shekara ta 1440 bayan Hijira. Mun ci dabino, mun kurɓi ruwa, kuma muka yi addu’ar shan-ruwa: *Zahabaz Zama’u, Wab Tallatil Uruuq, Wa Thabatal Ajru in shaa’al Laah* kafin mu fita zuwa sallar Maghrib a masallacin farko a layinmu: Layin Masallaci, Sabon Kawo Kaduna. Bayan sallame sallar Magrib sai liman ya miƙe, ladan kuma ya fara tayar da iƙamar sallar isha’i, da manufar a haɗa sallolin kenan, *Jam’u-Taqdeem.* A nan ne sai wasu mutane da suke sallah a wajen masallacin suka fara faɗin: *Ba hadari fa!* *Ba ruwan sama fa!* Amma liman bai saurare su ba, har aka kammala sallar. Sannan ko da aka sallame sallar ma bai ce komai a kan wannan matsalar ba. Don haka, na ga ya dace in yi amfani da wannan kafar in ce wani abu ko da a taƙaice a kan mas’alar. 1. Haɗa salloli biyu da suka yi tarayya a lokaci (Azahar da La’asar ko kuma Magrib da Ish...