Skip to main content

MAI DOKAR BACCI

A jihar Kaduna idan akwai wanda zamuce ya kawo korona bai wuce gwamna El-rufai, domin shine wanda aka fara samu da ita.


A jihar Kaduna ne gwamnan ya hana musulmai sallah tsawon wata 4.


A jihar Kaduna ne gwamnan ya hana kiristoci zuwa coci tsawon wata 4.


Har yanzu a jihar ne musulmai basu zuwa khamsu salawat da aka saba guda biyar, kuma har yanzu a jihar ne ya hana buɗe coci a ranar Saturday.


A tsakiyan faruwar hakan, gwamnan yace bazaije masallaci ba domin ya tsufa kada korona ta kamasa.


A lokacin ne gwamna ya bude masallacin juma'a da coci ranar Sunday tare da sharaɗin Social distance.


A lokacin ne kuma gwamnan da takwarorinsa suka haɗa gangamin taron kamfen na mutane sama da dubu goma.


Anya gwamnan Kaduna ba amso kwangilar rusa addinai yayi ba kuwa?


Koma dai menene Allah na nan fir'auna ma yayi ya wuce sai dai tarihi.


✍🏿

Muneer Yusuf Assalafy

10/08/2020

Comments

Popular posts from this blog

BARKA DA HUTUN ƘARSHEN MAKO

 BRANCOSIYYA HALARCI Alhaji Auwal Branco tare damu masoyansa, munawa Al'umma Barka da ƙarshen mako. Allah ya cikawa kowa burinsa. Muyi Branco da farar Zuciya #Branco2020 Muneer Yusuf Assalafy 08/08/2020

NASARA DAGA ALLAH

TSARIN MU NA KADUNA 'Ya'yan Jam'iyyar PDP na Zone 2 sun gamsu da riqon Shehu Giant shiyasa suke cewa so ✌ ne. Kaf matasan PDP dake Kaduna sun gamsu da Hon Aliyu Bello, hakan tasa muke cewa PDP Youth leader dan bello so ✌ ne. 'Yan PDP na Kaduna North Mun gamsu Mun amin ce da sauyin shugabanci, hakan yasa mukace Branco mukeso domin ya cancanta. Kawo Constituency kuwa maganar Sa'eed Usman Gombe ake a ko ina, domin cancantarsa da nagartarsa. Badarawa/Malali ward ko san barka 'yan PDP sukeyi da wakilcin Zayyanu Sa'eed Malali. Allah ya bamu nasara Muneer Yusuf Assalafy Zonal Coordinator Northwest Atiku 2023 Project Rescue Nigeria 06/07/2020

HADA SALLAH SABODA RUWAN SAMA

*TAMBAYA TA 100*  *HAƊA SALLAH SABODA RUWAN SAMA*  _As-Salaam Alaikum,_ Ranar Asabar bayan faɗuwar rana muka kai ƙarshen azumi na 13 a wannan shekara ta 1440 bayan Hijira. Mun ci dabino, mun kurɓi ruwa, kuma muka yi addu’ar shan-ruwa: *Zahabaz Zama’u, Wab Tallatil Uruuq, Wa Thabatal Ajru in shaa’al Laah* kafin mu fita zuwa sallar Maghrib a masallacin farko a layinmu: Layin Masallaci, Sabon Kawo Kaduna. Bayan sallame sallar Magrib sai liman ya miƙe, ladan kuma ya fara tayar da iƙamar sallar isha’i, da manufar a haɗa sallolin kenan, *Jam’u-Taqdeem.* A nan ne sai wasu mutane da suke sallah a wajen masallacin suka fara faɗin: *Ba hadari fa!* *Ba ruwan sama fa!* Amma liman bai saurare su ba, har aka kammala sallar. Sannan ko da aka sallame sallar ma bai ce komai a kan wannan matsalar ba. Don haka, na ga ya dace in yi amfani da wannan kafar in ce wani abu ko da a taƙaice a kan mas’alar. 1. Haɗa salloli biyu da suka yi tarayya a lokaci (Azahar da La’asar ko kuma Magrib da Ish...