*TAMBAYA TA 100*
*HAƊA SALLAH SABODA RUWAN SAMA*
_As-Salaam Alaikum,_
Ranar Asabar bayan faɗuwar rana muka kai ƙarshen azumi na 13 a wannan shekara ta 1440 bayan Hijira. Mun ci dabino, mun kurɓi ruwa, kuma muka yi addu’ar shan-ruwa: *Zahabaz Zama’u, Wab Tallatil Uruuq, Wa Thabatal Ajru in shaa’al Laah* kafin mu fita zuwa sallar Maghrib a masallacin farko a layinmu: Layin Masallaci, Sabon Kawo Kaduna. Bayan sallame sallar Magrib sai liman ya miƙe, ladan kuma ya fara tayar da iƙamar sallar isha’i, da manufar a haɗa sallolin kenan, *Jam’u-Taqdeem.* A nan ne sai wasu mutane da suke sallah a wajen masallacin suka fara faɗin: *Ba hadari fa!* *Ba ruwan sama fa!* Amma liman bai saurare su ba, har aka kammala sallar. Sannan ko da aka sallame sallar ma bai ce komai a kan wannan matsalar ba. Don haka, na ga ya dace in yi amfani da wannan kafar in ce wani abu ko da a taƙaice a kan mas’alar.
1. Haɗa salloli biyu da suka yi tarayya a lokaci (Azahar da La’asar ko kuma Magrib da Isha’i) ya halatta a wurin malamai, ko a halin tafiya ne ko kuma a halin zaman-gari. Kuma ko *Jam’u-Taqdeem* ne, watau: Haɗa sallolin biyu a lokacin sallar farko; ko kuma *Jam’u-Ta’kheer,* watau: Haɗa su a lokacin sallar ƙarshe, duk ya halatta.
2. Larurorin da suke halatta a haɗa salllolin sun haɗa da: *Tafiya* , da *ruwan-sama* , da *rashin lafiya* , da *tsoro,* da *iska* ko *sanyi* mai tsanani, da kuma duk wata *larura* da ka iya takura wa mutum ta sanya shi ya shiga cikin ƙunci idan ya yi ƙoƙarin yin sallolin kowacce a kan lokacinta. Kamar likita da zai shiga tiyata, ko kurtun soja ko ɗan sanda da zai shiga filin fareti, ko ɗalibin da zai shiga ɗakin jarabawa, ko matar da ke tsoron lalacewan kayan girkinta, da makamantansu. Duk waɗannan ya halatta su haɗa sallolinsu a farko ko a ƙarshen lokutan sallolin, idan sun yi buƙata.
3. Idan haɗa sallar saboda ruwan sama ne, ko sanyi ko duhu ko taɓo da makamantan haka, malamai sun ce ba za a haɗa ba sai in a masallaci ne. Don haka, wanda ke sallah a cikin gida ko a rumfar kasuwa kamar mata da waɗanda ba su samu daman zuwa masallaci ba, ba za su haɗa a inda su ke ba. Sai su bari sai bayan lokacin sallar ta-biyu ya shiga sai su sallace ta.
4. Yadda ake haɗa sallolin shi ne: Za a yi kiran sallar farko a farkon lokacinta, sannan a tayar da iƙamarta a sallace ta yadda aka saba. Da zaran an yi sallama sai kuma a sake tayar da iƙamar sallah ta biyu, ba tare da yi mata kiran sallah ba. Sai ita ma a sallace ta yadda aka saba. Wannan shi ne *Jam’u-Taqdeem.*
5. Idan kuwa *Jam’u-Ta’kheer* ne, to ba za a yi sallar farko a lokacinta ba. Bari za a yi sai lokacin sallah ta-biyu ya shiga sai a kira sallah, a tayar da iƙamar ta farkon, a sallace ta. Bayan sallama sai kuma a tayar da iƙamar ta biyun, ita ma a sallace ta.
6. Idan a masallaci ne liman shi ke da iko ko daman haɗa sallolin, kuma ba sai ya gaya wa mamu cewa zai haɗa ba, domin a lokacin da Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya haɗa sallolin Azahar da La’asar a *Arfa,* da kuma Maghrib da Isha a *Muzdalifah* bai gaya wa Sahabbai _(Radiyal Laahu Anhum)_ cewa zai haɗa ba, kamar yadda bai gaya musu cewa ƙasaru zai yi ba. Don haka, malamai suka ce niyyar haɗa sallar ba sharaɗi ne sai an yi ta a lokacin kabbarta sallar farko ba.
7. Kuma idan ba a samu dalilin haɗa sallolin ba sai a bayan sallame sallar farko, to duk da haka dai ya halatta a haɗa ta da sallah ta biyun.
8. Sannan kuma ba dole ne sai an samu jerantawa a tsakanin sallolin guda biyu ba. A kan haka, in da zai yi sallar farko a gida ko a wani masallaci, to zai iya zuwa wani masallacin ya haɗa sallar ta biyu, kuma ta yi.
9. Mamu ba su ne ke da hurumin takura wa liman a kan sai ya haɗa musu sallah ba, ko kuma su hana shi haɗawa, kamar yadda yake aukuwa a wasu masallatai. Haka kuma ba ladan ne ke da ikon miƙewa ya fara tayar da iƙama ba tare da jiran umurni ko ishara daga liman ba.
In dai shi liman da kansa ya ga dacewar ya haɗa sallar, shi zai nuna hakan kuma sai a miƙe a haɗa. In kuma bai ga hakan ba shikenan ba za a matsa masa lallai sai ya haɗa ba. Ana iya fita daga masallaci a tafi gida a bayan sallah ta-farko. Idan kuma lokacin sallah ta-biyu ya yi kuma aka ga fitowa zuwa sallar zai yi wa jama’a tsanani, sai ladan ya kira sallah a Masallacin kuma ya faɗa wa jama’a cewa: *Ku yi sallah a gida!* Wannan ma Sunnah ce.
10. Ba daidai ba ne, abin da wasu suke yi: Da zaran sun ga ladan ya miƙe za a haɗa sallar, sai su kuma su tashi su fice daga masallacin ba da wani uzuri ba! Wannan ba Sunnah ba ne. Abin da aka koyo daga magabata shi ne: Ibn Umar _(Radiyal Laahu Anhumaa)_ yana tsayawa ya haɗa sallah tare da limamai a lokacin da suke haɗawar saboda ruwan-sama da makamancinsa. Yawancin masu fitan nan da wuya su samu yin sallah ta-biyu a cikin jam’i. Yawanci su kaɗai suke yin ta a gida!
11. Bayan an gama haɗa sallolin ko mutum zai iya miƙewa nan-take ya kawo Wutrinsa? Abin da muka fi natsuwa da shi shi ne: Hakan bai kamata ba. Domin larurar sallah tare da jama’a ce ta sa aka ba da damar haɗa sallolin a farkon lokaci. Amma sallolin nafila na bayan Isha’i da sauran salloli da Wutri da ma ba a masallaci ake yinsu ba, a gida ya kamata a yi su. Don haka, sai mutum ya bar su har sai ya koma gida a bayan lokacin Isha’in ya shiga, sai ya yi.
12. Amma maganar da wasu ke cewa: Wai idan mutum ya zauna a masallacin har lokacin sallah ta-biyu ya shigo to sai ya sake yinta, wannan ma ba daidai ba ne. *Domin ai bai halatta a maimaita wata sallah ɗaya a rana ɗaya sau biyu ba,* sai da larura. Shiyasa malamai suka ce: In da larurar da ta sa su haɗa sallolin za ta kau a halin lokacin sallah ta-biyu bai shiga ba, duk da haka sallarsu ta yi, ba za su maimata ta ba.
A ƙarƙashin wannan, ana iya haɗa sallolin sannan kuma waɗanda su ke cikin masallacin su yi sallar *Asham* ko *Tarawihi* idan lokacinta ya yi. Haka kuma waɗanda suka fita zuwa gida ma suna iya komowa a yi tare da su, musamman idan larurar da ta sa aka haɗa sallolin a farko ta kau. Kamar dai yadda ake iya cigaba da karatu irin na tsakanin Magriba da Isha’i, ga ɗalibai a cikin masallacin yadda aka saba, a bayan an haɗa sallolin.
Allaah ya ƙara mana kyakkyawar fahimta a cikin addininmu.
_Wal Laahu A’lam._
_Wa Sallal Laahu Alaa Nabiyyinaa Wa Alihi Wa Sahbih._
Muhammad Abdullaah Assalafiy,
Markazu Ahlil-Hadeeth,
Kaduna.
01/06/2019
10: 54pm.

Allah ya saka da alkhairi
ReplyDelete