TAMBAYA TA 101
ƘWAYOYIN SUPPLEMENTS, DA AUREN MAZINACI
As-Salaam Alaikum,
Ina da tambayoyi guda biyu ne:
1. Menene hukuncin shan ƙwayoyin supplements masu ƙara hormones na mace, saboda ta samu kyawun fatar jiki da kyawun nono da kyawun gashin kanta?
2. Menene hukuncin auren wanda aka san mazinaci ne tun kafin a ƙulla auren?
AMSA A101
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.
[1] Irin wannan nau’in kwalliya ya sha bamban da irin wanda muka yi bayaninsa a tambaya ta 029 a baya. Domin wancan ya shafi shafe-shafe ne masu janyo sauye-sauye a bayan fatar jiki kawai, wannan kuma ya shafi sauya tunani ko tsarin gudanar da ayyukan jikin ne tun daga injunan cikin jikin, abin da zai janyo sauye-sauyen su zama na dindindin a jikin.
Bincike ya nuna cewa: Irin waɗannan ƙwayoyi ko allurori ko magunguna na zamani da ake amfani da su, yawanci ba su rasa abin da ake kira ‘side-effect’, watau: Wani ta’adi da suke janyowa ga jiki bayan ɗan amfanin da suke bayarwa. To, shin ko an binciki girman wannan ta’adin an tabbatar ba wani abin damuwa ba ne? Ko kuwa dai mai girma ne da ba zai yiwu a runtse-ido, a manta da shi ba? Idan kuma ba a iya bincikawa ba, ko kuma ba a iya ganowa ba, meyasa ba za a yi haƙuri kawai a zauna lafiya ba?! Musamman dayake a kwanan baya ga wata mace an nuna hotonta a Facebook da WhatsApp wadda ta je neman a yi mata irin wannan kwaskwariman don a ƙara girman mazaunanta, amma kuma sai ga wurin ya kwakkwaɓe, ya ruɓe, ya fara zagwanyewa!!
Sannan kuma wannan mai tambayar fa ba wai kwata-kwata ba ta da kyawun jiki ko kyawun nono ko kyawun gashi ba ne. A’a, tana da su. Amma dai so kawai ta ke ta ƙara samun mafi kyau. Meyasa ba za ta iya yin haƙuri da halin da Allaah ya halicce ta a kai ba? Kuma meyasa ba za ta gode wa Allaah Ta’aala a kan irin siffar asali da ya halicce ta a kai ba? Alhali kuma idan da za ta yi nazari da za a ga cewa a matsayinta ta fi wasu mata irinta kyawun waɗannan abubuwan?!
A ƙarshen Tambaya ta 029 a kan Zaƙewa Wurin Kwalliya mun ambaci cewa:
‘Hana yin amfani da waɗansu daga waɗannan abubuwa ya zo a cikin nassoshi sahihai sarihai a fili ƙarara, waɗansu kuma an fitar da hukuncinsu ne daga gamammun ƙa’idojin shari’a masu hana a yi amfani da su, kamar cewa suna jawo lahani ko ta’adi ga lafiyar jiki, ko kuma kamar cewa su koyi ne da kafirai. Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
مَنْ تَشَبَّهَ بِقَوْمٍ فَهُوَ مِنْهُمْ
Duk wanda ya kamantu da wasu mutane, to yana tare da su.
Har zuwa inda muka ce:
‘Wata kuma ta ce: Tana yin irin wannan ado da kwalliyan ne domin ta burge mijinta, ta ƙara janyo shi gare ta, ta hana shi kallon wasu mata a waje, musamman dayake akwai mata kafirai da fasiƙai da suke amfani da hakan suna ɗauke hankulan maza?
Amsa a nan sai a ce:
1. Wannan dai ba dalili ba ne, kuskure ne babba. Wai shi wannan mijin wane irin musulmi ne da ayyukan saɓon Allaah da kafirai da fasiƙai suke tafkawa yake burge shi? Wane irin musulmi ne haka da ya zama cewa kyakkyawar kwalliyar da shari’ar musulunci ta halatta wa matarsa ba ta burge shi ba, sai irin wadda shaiɗan ya ƙawata wa mabiyansa ne yake so?!
2. Kuma ba amfani da irin waɗannan kayayyakin kwalliyan a cikin gidaje domin wai a burge mazaje ne a yau ya haifar da abin da ya zama ruwan-dae ba? Inda ake ganin yaran mata da ’yan mata suna amfani da su a wajen gidajensu, suna bayyanawa ga samarinsu da sauran waɗanda ba muharramansu ba?! Kuma ga shi nan kullum abin sai ƙara haɓaka yake yi, duk kuwa da wa’azi da gargaɗin da Malaman Sunnah suke ta yi?! Waɗansu ashararan ma nema su ke Malamai su halatta musu amfani da waɗannan kayayyakin!!
3. A taƙaice dai, ko da an samu mijin da yake sha’awar waɗannan kayayyakin kwalliyan, kuma har yake sayo su domin matarsa ta yi amfani da su, abin da ya fi a fahimtarmu a yanzu shi ne, bai kamata ta yarda ta yi masa biyayya a kan haka ba, saboda maganar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da ya ce:
لَا طَاعَةَ لِمَخْلُوقٍ فِي مَعْصِيَةِ الْخَالِقِ
Babu biyayya ga wani halitacce a cikin saɓon Allaah Mahalicci
A nan kuma ana iya ƙarawa da…
4. Menene fa’idar burge miji ko janyo hankalinsa gare ki a cikin abin da a ƙarshe yana iya janyo miki matsalar rashin lafiyar da za ta sa shi kansa da sauran jama’a ma su ƙyamace ki, kamar idan jikinki ya fara zagwanyewa yana ruɓewa?!!
Allaah ya ƙara mana ilimi mai amfani.
[2] Amma game da hukuncin auren mazinaci, da farko dai:
Hukuncin da Shari’ar Musulunci Mai Adalci ta yanke musu (mazinata) shi ne: Idan ba su yi aure ba a yi wa kowane ɗaya daga cikinsu buloli guda ɗari a gaban jama’ar musulmi, ba tare da nuna wani tausayi gare su ba, kamar yadda ya ambata a cikin Suratun Nuur.
Idan kuwa dukkansu ko ɗayansu ya taɓa yin aure, to sai a ƙara masa da jefewa da duwatsu har sai ya mutu, kamar yadda Sunnah Sahihiya ta nuna.
Amma game da maganar auren mazinata da wanda ba mazinaci ba, a asali bai halatta ba. Allaah ya ce:
Mazinaci ba ya yin aure sai da mazinaciya ko mushirika, kuma mazinaciya ba mai aurenta sai mazinaci ko mushiriki, kuma an haramta wannan ga muminai.
(Surah An-Nuur: 3)
Sai dai kuma auren yana halatta idan an cika waɗansu sharuɗɗa:
Da farko: Sai sun tuba tuba ta gaskiya a bisa sharuɗɗan da Malamai suka shimfiɗa, tun kafin mahukunta su samu iko a kansu. Domin a inda Allaah yake magana a kan masu laifin yin tarayya da Allaah, da kisan-kai, da yin zina cewa: Ana ruɓanya musu azaba a Ranar Ƙiyama, kuma za su dawwama a cikinta, sai kuma ya ce:
Sai dai wanda ya tuba, kuma ya yi imani, kuma ya aikata aiki na-gari; to irin waɗannan ne Allaah yake sauya musu munanan ayyukansu su koma kyawawa, kuma Allaah ya kasance Mai Yawan Gafara ne, Mai Yawan Tausayi.
(Surah Al-Furqaan: 70)
Na-biyu: Idan kuma mazinaciyar mace ce, to sai ta yi istibra’i, watau ta zauna na tsawon lokacin da za a tabbatar cewa babu jariri a cikin mahaifarta. Watau sai ta yi haila ko da sau ɗaya ne. Idan kuma ya tabbata cewa tana da ciki daga zinar, to ba zai yiwu a ɗaura auren ba sai bayan ta haihu, saboda maganar Allaah Ta’aala cewa:
Kuma masu cikunna iddarsu ita ce su haife cikinsu.
(Surah At-Talaaq: 4)
Wal Laahu A’lam.
01/06/2019
3: 31
*sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
Majlisin sunnah
08164363661

Comments
Post a Comment