Skip to main content

MASU RABA QAFA A CIKIN ADDINI

TAMBAYA TA 099

MASU RABA-ƘAFA A CIKIN ADDINI

As-Salamu Alaikum,

Malam, wata matsala ce da ta zama kamar ruwan-dare a wasu sassa ko yankunan ƙasar nan: Mutum ya ce ya raba-ƙafa a cikin addini, watau yana zuwa masallaci kuma yana zuwa coci, wai yana gudun kar ya zo wanda ya bi a nan ba shi ne zai haye ba a lahira! Wai shin yaya matsayin irin waɗannan mutanen?

AMSA A099

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Irin waɗannan in dai ba masu taɓin-hankali ba ne, to manyan jahilai ne. Ba su fahimci komai ba a cikin addinin musulunci. Domin Kalmar shahada wacce da ita ake shiga addinin Musulunci ta fayyace komai. Shaidawar da bawan Allaah ya yi cewa: Babu abin bautawa da gaskiya sai dai Allaah shi kaɗai, ba shi da abokin tarayya, wannan abin da yake nufi shi ne: Mutum ya amince ne tun daga zuciyarsa har bakinsa zuwa ga gaɓoɓinsa cewa: Allaah Ta’aala Maƙagin halittar sammai da ƙasa, da duk abin da ke cikinsu, da abin da ke a tsakaninsu, wanda kuma yake gudanar da al’amuransu, guda ɗaya ne, shi ne Allaah Tabaaraka Wa Ta’aala: Ba shi da farko, ba shi da ƙarshe, kuma ba shi da iyaye, ko mata, ko ɗa, ko wani abokin tarayya. Don haka, shi kaɗai ne kaɗai abin bauta, ban da duk wanda ba shi ba daga cikin Mala’iku da Annabawa da Manzannin Allaah. Ballantana sauran halittun da ba su kai su daraja ba, daga cikin itatuwa da duwatsu da dabbobi da tsuntsaye da sauran shaiɗanun mutane da aljanu da sauransu!

Amma a cikin addinin kirista kuwa, sun ɗauki Allaah a wurinsu guda ɗaya ne amma a cikin alloli guda uku: Uba da Ɗa Ruhi mai Tsarki! Wannan kuwa wani babban zunubi ne mai Girma a mahangar addinin Musulunci. Domin Allaah bai yarda da wannan gamayyar ko haɗin-gwiwar ba, ya ƙyamace shi, kuma ya kafirta duk mai amincewa da wannan aƙidar. Allaah ya ce:

Haƙiƙa! Waɗanda suka ce: Allaah shi ne Masihu Ɗan Maryam sun kafirta, kuma Masihun cewa ya yi: Ya ku Bani-Isra’ila! Ku bauta wa Allaah Ubangijina kuma Ubangijinku. Kuma lallai duk wanda ya yi tarayya da Allaah, to tabbas! Allaah ya haramta masa Aljannah, kuma makomarsa ita ce Wuta, kuma azzalumai ba su da wasu mataimaka!

Haƙiƙa! Waɗanda suka ce: Allaah shi na-ukun alloli uku ne sun kafirta! Kuma babu wani abin bautawa sai dai abin bauta guda ɗaya (shi ne: Allaah). Kuma idan ba su ciru daga abin da suke faɗi ba, to lallai azaba mai raɗaɗi za ta shafi waɗanda suka yi kafircin daga cikinsu!
(Surah Al-Maa’idah: 72-73)

Sannan kuma jingina wa Allaah ɗa shi ne mafi munin zagi gare shi Subhaanahu Wa Ta’aala. Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya faɗa a cikin hadisin da Al-Imaam Al-Bukhaariy (4482) ya fitar daga riwayar Ibn Abbaas (Radiyal Laahu Anhumaa) cewa:

  قَالَ اللَّهُ : كَذَّبَنِى ابْنُ آدَمَ وَلَمْ يَكُنْ لَهُ ذَلِكَ ، وَشَتَمَنِى وَلَمْ يَكُنْ لَهُ ذَلِكَ ، فَأَمَّا تَكْذِيبُهُ إِيَّاىَ فَزَعَمَ أَنِّى لاَ أَقْدِرُ أَنْ أُعِيدَهُ كَمَا كَانَ ، وَأَمَّا شَتْمُهُ إِيَّاىَ فَقَوْلُهُ لِى وَلَدٌ ، فَسُبْحَانِى أَنْ أَتَّخِذَ صَاحِبَةً أَوْ وَلَدًا
Allaah ya ce: ‘Ɗan Adam yana ƙaryata ni, kuma hakan bai kamace shi ba. Sannan kuma yana zagi na, hakan kuma bai kamace shi ba. Amma ƙaryata ni shi ne: Riyawarsa cewa wai ba ni da ikon sake mayar da halittarsa kamar yadda ya kasance kafin mutuwarsa. Zaginsa gare ni kuwa shi ne: Cewa da ya yi wai ina da ɗa! Na tsarkaka daga in riƙi mata ko kuma ɗa!’
Kai! Faɗin cewa Allaah Ta’aala yana da ɗa wata mummunar magana ce da ta kusa ta ruguza rayuwar duniyar nan! Allaah Ta’aala ya ce:


Sama ta yi kusa ta kekkece saboda shi, kuma ƙasa ta tsattsage, kuma duwatsu su rididdige; saboda sun jingina ɗa ga Allaah Mai Rahama
(Surah Maryam: 90-91)

To, ta yaya wanda ya san wannan a Musulunci zai taɓa yin tunanin samun tsira a hanyar masu faɗin irin waɗannan munanan maganganun ga Allaah Tabaaraka Wa Ta’aala?!!

Don haka, abin da ya wajaba ga duk wanda ya sani shi ne: Ya karantar da irin waɗannan mutanen sahihin addinin musulunci. Kuma kar a kuskura a mayar da maganganunsu abin dariya ko raha. Domin ko kusa abin ba na dariya ko annashuwa ba ne. Laifin kan iya shafar waɗanda suka yi sakaci wurin karantar da su ma. Allaah ya kyauta.

Amma game da matsayinsu a lahira, wannan kam yana wurin Allaah Ta’aala ne Masanin ɓoye da bayyane na dukkan al’amura. Idan a haƙiƙa iyakan ilimin mai irin wannan ra’ayin kenan, kuma tsoron Allaah ne manufarsa ga hakan, to zai iya yiwuwa Allaah ya yafe masa, kamar yadda ya yafe wa wanda ya yi wasiyya ga ’ya’yansa cewa: Bayan mutuwarsa su ƙona gawarsa, kuma su sheƙe tokar a cikin iska, don gudun kar Allaah ya kama shi!
Idan kuma shegantaka ce da sakaci wurin neman gaskiya, to wannan al’amarinsa a fili ya ke.

Allaah ya kiyaye!

Wal Laahu A’lam.
31/5/2019
6: 40am

*Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*

Majlisin sunnah
08164363661

Comments

Popular posts from this blog

HADA SALLAH SABODA RUWAN SAMA

*TAMBAYA TA 100*  *HAƊA SALLAH SABODA RUWAN SAMA*  _As-Salaam Alaikum,_ Ranar Asabar bayan faɗuwar rana muka kai ƙarshen azumi na 13 a wannan shekara ta 1440 bayan Hijira. Mun ci dabino, mun kurɓi ruwa, kuma muka yi addu’ar shan-ruwa: *Zahabaz Zama’u, Wab Tallatil Uruuq, Wa Thabatal Ajru in shaa’al Laah* kafin mu fita zuwa sallar Maghrib a masallacin farko a layinmu: Layin Masallaci, Sabon Kawo Kaduna. Bayan sallame sallar Magrib sai liman ya miƙe, ladan kuma ya fara tayar da iƙamar sallar isha’i, da manufar a haɗa sallolin kenan, *Jam’u-Taqdeem.* A nan ne sai wasu mutane da suke sallah a wajen masallacin suka fara faɗin: *Ba hadari fa!* *Ba ruwan sama fa!* Amma liman bai saurare su ba, har aka kammala sallar. Sannan ko da aka sallame sallar ma bai ce komai a kan wannan matsalar ba. Don haka, na ga ya dace in yi amfani da wannan kafar in ce wani abu ko da a taƙaice a kan mas’alar. 1. Haɗa salloli biyu da suka yi tarayya a lokaci (Azahar da La’asar ko kuma Magrib da Ish...

NASARA DAGA ALLAH

TSARIN MU NA KADUNA 'Ya'yan Jam'iyyar PDP na Zone 2 sun gamsu da riqon Shehu Giant shiyasa suke cewa so ✌ ne. Kaf matasan PDP dake Kaduna sun gamsu da Hon Aliyu Bello, hakan tasa muke cewa PDP Youth leader dan bello so ✌ ne. 'Yan PDP na Kaduna North Mun gamsu Mun amin ce da sauyin shugabanci, hakan yasa mukace Branco mukeso domin ya cancanta. Kawo Constituency kuwa maganar Sa'eed Usman Gombe ake a ko ina, domin cancantarsa da nagartarsa. Badarawa/Malali ward ko san barka 'yan PDP sukeyi da wakilcin Zayyanu Sa'eed Malali. Allah ya bamu nasara Muneer Yusuf Assalafy Zonal Coordinator Northwest Atiku 2023 Project Rescue Nigeria 06/07/2020

MAI DOKAR BACCI

A jihar Kaduna idan akwai wanda zamuce ya kawo korona bai wuce gwamna El-rufai, domin shine wanda aka fara samu da ita. A jihar Kaduna ne gwamnan ya hana musulmai sallah tsawon wata 4. A jihar Kaduna ne gwamnan ya hana kiristoci zuwa coci tsawon wata 4. Har yanzu a jihar ne musulmai basu zuwa khamsu salawat da aka saba guda biyar, kuma har yanzu a jihar ne ya hana buɗe coci a ranar Saturday. A tsakiyan faruwar hakan, gwamnan yace bazaije masallaci ba domin ya tsufa kada korona ta kamasa. A lokacin ne gwamna ya bude masallacin juma'a da coci ranar Sunday tare da sharaɗin Social distance. A lokacin ne kuma gwamnan da takwarorinsa suka haɗa gangamin taron kamfen na mutane sama da dubu goma. Anya gwamnan Kaduna ba amso kwangilar rusa addinai yayi ba kuwa? Koma dai menene Allah na nan fir'auna ma yayi ya wuce sai dai tarihi. ✍🏿 Muneer Yusuf Assalafy 10/08/2020