TAMBAYA TA 101 ƘWAYOYIN SUPPLEMENTS, DA AUREN MAZINACI As-Salaam Alaikum, Ina da tambayoyi guda biyu ne: 1. Menene hukuncin shan ƙwayoyin supplements masu ƙara hormones na mace, saboda ta samu kyawun fatar jiki da kyawun nono da kyawun gashin kanta? 2. Menene hukuncin auren wanda aka san mazinaci ne tun kafin a ƙulla auren? AMSA A101 Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah. [1] Irin wannan nau’in kwalliya ya sha bamban da irin wanda muka yi bayaninsa a tambaya ta 029 a baya. Domin wancan ya shafi shafe-shafe ne masu janyo sauye-sauye a bayan fatar jiki kawai, wannan kuma ya shafi sauya tunani ko tsarin gudanar da ayyukan jikin ne tun daga injunan cikin jikin, abin da zai janyo sauye-sauyen su zama na dindindin a jikin. Bincike ya nuna cewa: Irin waɗannan ƙwayoyi ko allurori ko magunguna na zamani da ake amfani da su, yawanci ba su rasa abin da ake kira ‘side-effect’, watau: Wani ta’adi da suke janyowa ga jiki bayan ɗan amfanin da suke bayarwa. To, shin ko an binciki girma...