N-POWER KO RASHIN AIKI KO MUTUWAR ZUCIYA? Hukumar N-power sun qiyasta mutum 100 na rijista duk second daya. Hakan yana faruwa ne sbd qarancin rashin aikinyi a Lafjeriya, da yawan wadanda suka gama jami'a basu da abinyi, hakan tasa aka bude N-power domin su rinqa samun albashi da zai rage musu talauci. Ga matashin da yasan abinda yake, sam bai kamata ya bari zuciyar sa ta mutu ba wajen neman N-power musamman ga 'yan sakandare. Matasa kada ku bari zuciyar ku ta mutu wajen neman N-power, ku tashi ku nema na kanku ko zaku rufawa kanku asiri. Abin takaici shine hatta 'yan sakandare ma zuciyar su ta mutu suna jiran su samu na gwamnati, a lokacin da abokansu suke aikin hannu suna samun manyan kudi. Kaba kanka amsa ga wadannan tambayoyin yakai dan sakandare da ka cike N-power 1. Shin kudin da zasu baka zai cireka a talauci? 2. Shin dubu goma da za a baka duk Wata zai isheka aure? 3. Dubu goma da za a baka zai Isa kasai gida? 4. Dubu goma da za a baka zai isa Kas...